Somaliya
Kungiyar kare hakkin Bil adama ta Human Rights Watch ta yi zargin cin zarafin ‘Yan Somalia
Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch, ta yi zargin cewar ‘Yan bindiga a kasar Somalia suna cin zarafin mutanen da suka rasa matsuguninsu, har ma da yiwa matansu fyade.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotan da kungiyar ta fitar ya ruwaito wata mata da ta yi bayanin cewar, wasu ‘Yan bindiga sun yi mata fyade a sansanin da ke Mogadishu.
Daraktan kungiyar, David Mepham ya kuma zargi masu kula da su a sansanin da sace abincin da ake baiwa ‘Yan gudun hijiran da kuma kayan agaji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu