Dakarun Mali 63 tare da na yan tawaye 600 suka rasa rayukansu yanzu haka a yakin kasar
Rundunar Sojin kasar Mali, tace an kashe mata dakarun ta 63, yayin da aka kuma kashe Yan Tawaye 600 tun bayan kaddamar da yakin kasar a watan Janairu.
Wallafawa ranar:
Kakakin sojin, Lt Col Souleyman Maiga, ya kuma ce an kashe sojojin kasashen Togo, Burkina Faso Fransa da Chadi, daga cikin sojojin da suka kai musu dauki.
A yayinda dakarun Kasar Britaniya 40 suka isa kasar Mali, dan horar da sojojin kasar, kan yadda zasu gudanar da aiyukan su, sakamakon matsalar Yan Tawayen da aka samu.
Rundunar sojin Britaniya tace, sojoji 21 sun isa Bamako, yayin da wasu 29 zasu same su can, kamar yadda kungiyar kasashen Tuari ta bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu