Kasashen Tsakiyar Afirka sun yi watsi da Djotadia a matsayin shugaba
Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya ce taron shugabannin kasashen da ke Tsakiyar Afirka, ya ki amincewa da shugaban ‘Yan Tawayen Seleka Michel Djotodia, wanda ya kwaci mulki da karfi a matsayin Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Wallafawa ranar:
Bayan taron da shugabannin suka yi a birnin Ndjamena, shugaba Deby ya ce ba za su amince da Michel Djotodia ba, a matsayin jagora kasar.
Shugaban na Chadi ya ci da cewa, za’a kafa wani kwamitin fitattun mutanen kasar ne da zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya, kana kwamitin ne zai zabo shugaba, wanda zai shirya zabe a cikin watanni 18 da za su biyo baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu