Isa ga babban shafi
Turai

Tarayyar Turai za ta kara taimakawa kasashe masu fama da karancin abinci

Kungiyar Tarayyar Turai, ta ce za ta kara yawan kudaden tallafin da ta ke bai wa kasashen yankin Sahel inda yanzu haka fiye da mutane milyan 10 ne ke fama da matsalar karancin abinci.

Wani manomi na girbin amfanin gona a yankin Kanem na gabashin kasar Chadi
Wani manomi na girbin amfanin gona a yankin Kanem na gabashin kasar Chadi AFP PHOTO / OXFAM / IRINA FUHRMANN
Talla

Shugaban sashen bayar da agajin abinci na kungiyar Mista Claus Sorensen, wanda ya kai ziyarar aiki a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, ya bayyanawa mujallar Echo da ake bugawa a kasar cewa, daga cikin wadannan mutane fiye da milyan 10 da ke fama da yinwa, milyan 4 da rabi kananan yara ne, kuma milyan daya da rabi daga cikinsu, yanzu haka suna rayuwa ne a cikin matsanancin hali sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Daga shekarar bara zuwa bana, kungiyar ta Tarayyar Turai ta ware kudaden da yawansu ya kai Euro milyan 3,88 domin taimakawa kasashen yankin sakamakon karancin abincin da suke fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.