Isa ga babban shafi
Mali

‘Yan tawayen Mali sun ki amincewa da tayin ajiye makamai

‘Yan tawayen kasar Mali sun ki amincewa da bukatar kasar Faransa na su ajiye makaman su kafin zaben watan Yuli, inda suke cewa za su fafata har sai bayan ransu, kafin su bar sojin Mali su shiga inda suke rike da shi.

Dakarun Mali
Dakarun Mali AFP/ERIC FEFERBERG
Talla

Mataimakin shugaban ‘Yan Tawayen, Mamadou Djeri Maiga, ya ce Faransa na da hurumin tilastawa Gwamnatin Mali ta tattauna da su dan samu kwarya kwaryan ‘yancin Arewacin kasar.

Tun dai a watan Janairun wannan shekara ake ta fafatawa da tsakanin dakarun kasar Mali da ‘Yan tawayen kasar bayan dakarun Faransa sun tallafawa gwamnatin ta Mali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.