An kai harin bam a birnin Benghazi da ke gabashin Libya
Wani harin bam da ya faru a sanyin safiyar yau asabar a birnin Benghazi da ke gabashin kasar Libya ya haddasa mummunar barna ga wani gini, duk da cewa ba a samu asarar rayukan jama’a ba.
Wallafawa ranar:
Babban jami’in ‘yan sanda a yankin da lamarin ya faru mai suna Kanar Matar Mohammed, ya ce bam din ya fashe ne da misalin karfe 6 na safe agogon kasar, kuma yanzu haka suna kan gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen tayar da shi.
Ko a ranar talatar da ta gabata an kai harin bam a kan ginin ofishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Tripoli inda ya raunata mutane da dama. A can kuwa birnin Benghazi, ko a cikin makon da ya gabata wasu dauke da makamai sun kai hari a kan wani ofishin ‘yan sanda inda suka ‘yantar da mutane da dama da ke tsare a wurin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu