Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Sandan Najeriya sun tabbatar da sakin Mongunu da aka sace

‘Yan Sandan Najeriya sun tabbatar da sakin Tsohon Ministan Mai Shettima Ali Monguno da ‘Yan bindiga suka sace a garin Maiduguri Jahar Borno. Wata majiya tace an biya kudi Naira Miliyan 50 kafin a saki tsohon Ministan, kodayake babu wani cikakken bayani daga bakin ‘Yan sandan.

Dakta Shettima Ali Monguno
Dakta Shettima Ali Monguno
Talla

Babban jami’in ‘Yan sandan Jahar Borno Abdullahi Yuguda shi ne ya tabbatar da labarin sakin Ali Monguno. Amma tuni Abubakar Ali Monguno, ya shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa ‘yan bindigar sun bukaci a biya su kudi tun a ranar Juma’a kafin su saki Mahaifin shi.

00:42

Aliyu Tishaku

Tuni dai kungiyar Boko Haram ta nisanta kan ta da daukar alhakin yin garkuwa da tsohon Ministan kamar yadda Aliyu Tishaku ya kare kansu a hirar shi da RFI Hausa.

Yanzu haka, ‘Yan bindiga na fakewa da sunan Boko Haram su kai hare hare tare da aikata ta’asa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.