Jana’izar Farfesa Chinua Achebe
A yau Alhamis ake sa ran binne shahararren marubucin adabin nan, dan Nigeria Farfesa Chinua Achebe, da ya mutu a ranar 21 ga watan Maris din wannan shekarar a kasar Amurka, yana da shekaru 82.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Za a binne Chinua Achebe ne a garin shi na haihuwa, Ogidi da ke cikin karamar hukumar Idemili ta arewa, da ke jihar Anambra, a kudu maso gabashin kasar.
Achebe a lokacin rayuwarsa ya kyamaci cin hannci da rashawa, ya rubuta littatafai da dama, da suka hada da "Things fall Apart," "Arrow of God" da "No longer at ease," da kuma aka fassara wasu daga cikin su zuwa harsuna da dama a duniya.
Ana sa ran jiga jigan mutane, shugabanni da maruduta daga ciki da wajen kasar za su halarci bukin binne marubucin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu