Isa ga babban shafi
DRC Congo

Dakarun MDD za su ci gaba da zama a Congo

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, zasu kasance a Jamhuriyar Demokradiyar Congo cikin watanni biyu masu zuwa, a cewar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban kin Moon da ke ziyarar yankin.Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ban kin Moon a ya ziyarcin yankin Goma .Matakin na tura dakarun da suka kai akalla 3000 zuwa kasar, ya zo ne sanadiyar sabon rikicin da ya barke a yankin GomaDakarun sun kunshi ‘yan kasashen Tanzania, Malawi da kuma Afrika Ta Kudu da Majalisar ta tantance a watan Maris da ya gabata.Dakarun zasu marawa wadanda ke aiki a yanzu haka a can, da yawansu ya kai akalla dubu 17.Wannan shi ne karo na farko da Majalisar ta Dinkin Duniya ke hada irin wannan tawagar sojoji domin wanzar da zaman lafiya. Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim da ke tare da Ban ki Moon yayin wannan ziyarar, ya yi alkawarin bada agajin kudi, Dollar Amurka miliyon dubu daya, wajen ganin al’umar yankin sun anfana da kayayakin more rayuwa, da ke a matsayin wata dama ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.Duk da arzikin ma’adanan karkashin kasa, da jamhuriyar ta kongo ke da shi, kasar na layin kasashe da talauci ya yiwa katutu sanadiyar yaki da ya janyo asarar rayuka.Dakarun a cewar Ban, zasu kasance a jamhuriyar demokradiyar kongo cikin wata daya ko biyu masu zuwa.  

Sakatyare janar na MDD Ban Ki-moon tare da shugaban bankin duniya,  Jim Yong Kim a kasar Congo
Sakatyare janar na MDD Ban Ki-moon tare da shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim a kasar Congo REUTERS/Jonny Hogg
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.