Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Afrika

Za a rufe taron bikin cika Kungiyar Tarayyar Turai shekaru 50 da kafuwa

A yau Litinin za a rufe bukukuwan cikar Kungiyar Tarayyar Turai shekaru 50 da kafuwa bayan kwashe kwanaki biyu ana gudanar da bukuwan. An dai fara taron ne da tattaunawa da manyan matsalolin da kasashen nahiyar ke fama da su musamman ma yake-yaken basasa.  

Taron bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar Tarayyar Afrika
Taron bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar Tarayyar Afrika previous.presstv.ir
Talla

Daya daga cikin batutuwan da shugabannin suka kuma tuna tattaunawa har ila yau shi ne halin da ake ciki a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, wanda duk da cewa an cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnati da kuma ‘yan tawayen M23 a cikin watan Fabarairun da ya gabata, amma har yanzu ana ci gaba da samun hare-hare jefi jefi.

Shugaban kasar Tanzaniya, daya daga cikin kasashen da ke shirin aikewa da dakarunsu zuwa yankin da ke fama da rikici a Congo, Jakaya Kikwete, a lokcin taron ya ce ana samun ci gaba sosai a kokarin da Afirka ke yi don samar da zaman lafiya a wannan kasa da ta share tsawon shekaru tana fama da rikici.

Har ila yau a taron kasashen na Afrika Shugaban kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, ta ce maganar tsaro musamman na kan iyakokin da Liberia ke makwabtaka da su yana matukar muhimmaci.

"Batun zaman lafiya da tsaro abu ne mai matukar muhimmaci a gare mu, domin matsala ce da ta shafi kasashen yammaci afrika." Inji Sirleaf.

Shugabannin kasashen Rwanda da Uganda da kuma Angola sun yi wata ganawa ta bayan fage game da rikicin Congo, kuma Ministan harakokin wajen Angola, Georges Chicoty ya shaidawa RFI cewa dakarun Tanzania za su doshi Congo a cikin watan nan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.