Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Mandela ya fara samun sauki a cewar shugaba Jacob Zuma

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob zuma yace Tsohon shugaba Nelson Mandela ya fara samun sauki a kwanaki biyar da ya kwashe kwance a gadon Asibiti. Zuma ya tabbatar da haka ne a gaban ‘Yan Majalisun kasar yana mai godewa wadanda suka taimaka da Addu'a.

Shugaban Afrika ta Kudu  Jacob Zuma tare da Nelson Mandela
Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma tare da Nelson Mandela AFP PHOTO / GOVERNMENT COMMUNICATION AND INFORMATION SYSTEM / HO
Talla

“Muna farin ciki da wannan ci gaban da aka samu fiye da kwanakin baya” inji Shugaba Zuma.

Zuma wanda ke jawabi a dai dai lokacin ake cika shekaru 49 da yanke wa Mandela hukucin daurin rai da rai a gidan yari, ya kai ziyarar girmamawa ga shugabannin da suka gaji Mandela da sauran mutanen da suka yi zaman gidan yari tare da tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.