Isa ga babban shafi
Mali

Shugaban Mali bai yarda da wani sashe na yarjejeniya da ‘Yan tawaye ba

Masu shiga tsakanin sasanta ‘Yan tawayen Mali da gwamnati sun bar Ouagadougou zuwa Bamako domin mikawa shugaba Dioncounda Traore yarjejeniyar da suka cimma tsakanin bangarorin biyu a Burkina Faso.

Dioncounda Traoré, Shugaban riko a kasar Mali.
Dioncounda Traoré, Shugaban riko a kasar Mali. REUTERS/Adama Diarra
Talla

Wata majiya ta tabbatar wa Kamfanin dillacin Labaran Faransa cewa ministan harakokin wajen Burkina Faso Djibrill Bassole ya nufi Mali a cikin jirgin sama mallakar Majalisar Dinkin Duniya domin gabatar da yarjejeniyar da aka cimma tare da shi da akwai wakilan Majalisar Dinkin Duniya, da na Kungiyar kasashen Turai da kuma wakilan Faransa a tawagar.

Yarjejeniyar dai ta shafi hanyoyin da za’a samu gudanar da zabe a Kidal da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen Abzinawa. A ranar 28 ga watan Juli ne aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa bayan dakarun Faransa sun taimaka wajen karbe ikon Arewacin kasar da ya fada hannun Mayakan MUJAO da Ansar dine da suka kaddamar da Shari’ar musulunci.

kasar Mali dai na fatar komawa ga mulkin Demokradiya bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure a watan Maris din bara, to amma rahotannin baya bayan nan na nuni da cewa shugaban Dioncounda Traore ya ki amincewa da wani bangare na daftarin yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.