Isa ga babban shafi
Amurka-Afrika

Obama ya kammala ziyara a kasashen Afrika

Shugaban Amurka Barack Obama ya kammala ziyarar kasashe uku da ya kawo a kasashen Afrika a Tanzania bayan ya kai ziyara Senegal da Afrika ta Kudu domin inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen da Amurka. Amma rashin lafiyar Mandela ita ce ta shafe ziyarar Obama a Afrika ta Kudu.

Shugaban Amurka Barack Obama yana gaisawa da Shugaban Tanzania Jakaya Kikwete cikin dafifin Jama'a à Dar Es Salam.
Shugaban Amurka Barack Obama yana gaisawa da Shugaban Tanzania Jakaya Kikwete cikin dafifin Jama'a à Dar Es Salam. Cameron / Reuters
Talla

Obama ya kawo karshen Ziyararsa ne a Dar es Salaam inda ya samu tarba ta musamman daga daruruwan mutanen Tanzania. Kuma Obama ya kaddamar da wani aikin samar da hasken wutar Lantarki da aka kashe kudin Amurka Dala Biliyan Bakwai.

Ziyarar Obama dai na zuwa ne bayan takwaransa na China Xi Jinping ya kawo ziyara kasashen Afrika wadanda ke hamayyar kasuwaci da juna.

“Ina ganin Afrika a matsayin Nahiyar da za ta samu ci gaban tattalin arziki kuma Amurka tana fatar kasancewa abokiyar hulda” inji Obama.

Shugaban Tanzania, Jakaya Kikwete, yace Afrika tana bukatar Amurka, Amurka kuma tana bukatar Afrika saboda haka yadda kawai za’a habaka wannan dangantaka shi ne ta ziyartar juna.

Mista Kikwete, ya godewa Obama tare da neman Amurka za ta ci gaba da kasancewa abokiyar huldar Tanzania.

A kasar Afrika ta kudu, rashin lafiyar Mandela ita ce ta shafe muradun ziyarar Obama, wanda shugaban na amurka ya bayyana a matsayin jaruminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.