Isa ga babban shafi
Mali

An dage dokar ta-baci a Mali

Gwamnatin Mali ta dage dokar ta-baci da aka kafa tun a watan Janairu, domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na farko da za’a gudanar a ranar 28 ga watan Juli. Kamar yadda Jami’an tsaron kasar suka tabbatar.

Akwatunan zaben shugaban kasa a kasar Mali
Akwatunan zaben shugaban kasa a kasar Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

Tun a ranar 12 ga watan Janairu ne aka kafa dokar ta-baci a kasar Mali bayan Dakarun Faransa sun kaddamar da yaki domin kwato yankin arewaci daga hannun ‘Yan tawaye.

Dokar ta kunshi haramta gudanar da wani gangami ko taro da kuma zanga-zanga a saman tituna.

Dage dokar ta-bacin na zuwa ne bayan Kotun kundin tsarin Mulki ta tantance ‘Yan takara 28 da za su shiga takarar zaben shugaban kasa. Kuma hakan na zuwa ne bayan dakarun Mali sun samu kutsa kai a yankin Kidal da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen MNLA masu fafutikar kafa kasar AZAWAD.

Dakarun sun samu shiga Kidal ne karkashin yarjejeniyar da gwamnatin Mali da ‘Yan tawayen Abzinawa suka cim ma a kasar Burkina Faso a ranar 18 ga watan Juni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.