Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya kafa sabuwar gwamnati a Kudancin Sudan

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya nada sabuwar gwamnati bayan da ya rusa gwamnatin a cikin makon jiya amma har yanzu bai nada mataimakin shugaban kasa ba. Wasu daga cikin sabbin fuskoki da Salva Kir ya nada a cikin gwamnatin sun hada da mukamin ministan tsaro da ya danka a hannun gwamnan lardin Jonglei mai fama da rikici a gabacin kasar.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Talla

Sai dai mataimakinsa Riek Machar da kuma Pagan Amum wadanda aka tube daga mukamin sakataren jam’iyar mai mulkin kasar ba su dawo a cikin gwamnatin ba.

Har ila yau shugaban na Sudan ta Kudu ya aiwatar da wasu sauye sauye a cikin manyan ma’aikatu na kasar da hade wasu ma’aikatu wuri daya da kuma canzawa wasu ministoci zuwa wasu ma’aikatu na daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.