Isa ga babban shafi
Najeriya

An samu hasarar rayuka a Bama da Malam Fatori a Najeriya

Rundunar sojin Najeriya tace Mutane 35 ne suka mutu a wata Musayar wuta da suka yi da ‘Yan bindiga da ake zaton ‘Yan Boko Haram ne kuma yawancin wadanda suka mutu daga cikin ‘Yan bindigar ne a wasu biranen arewacin Najeriya.

Rundunar Sojin Najeriya.
Rundunar Sojin Najeriya. REUTERS/Stringer
Talla

Rikicin ya barke ne bayan kai wa sojoji da ‘Yan sanda hari a cewar Jami’an tsaron na Najeriya.

Jami’an tsaron sun ce Mambobin Boko Haram 17 ne suka kashe a musayar wutar da suka yi a garin Bama.

Yayin da kuma a garin Malam Fatori aka kashe ‘Yan bindiga 15, kuma duka hare haren sun faru ne a ranar Lahadi.

Biranen da aka kai harin dukkaninsu suna karkashin Jahar Borno ne da aka kafawa dokar ta baci domin farautar ‘yayan kungiyar Boko Haram.

Jami’an tsaron na Najeriya sun ce ‘Yan bindigar suna dauke ne da muggan Makamai da suka hada da bindigogi kirar AK 47 guda 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.