Isa ga babban shafi
Masar

Gwamnatin Masar ta sha alwashi watse gangamin ‘Yan uwa Musulmi

Firaminsitan kasar Masar Hazem al-Beblawi ya sha alwashin watse gangamin ‘Yan uwa Musulmi a birnin al Kahira bayan fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa an kasa samun maslaha a tattaunar da aka gudanar tsakanin wakilan kasashen waje da magoya bayan Morsi

Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi
Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi Reuters / Waguih
Talla

“Ba gudu ba ja da baya akan matakin watse Dandalin Rabaa da Nahda” a cewar Firaministan a kafar Talabijin din kasar.

Fadar Shugaban kasar Masar tace duk wani kudiri na diflomasiya da aka bi ya cutura tare da yin gargadi ga magoya bayan Morsi cewa zasu biya bashin abinda zai biyo baya.

A cikin Sanarwar da ta fito daga shugaban riko Adly Mansour tace kokarin da wakilan kasashen waje suka yi na tsawon kwanaki 10 ya kawo karshe.

Wakilai daga Amurka da kasashen Turai da  Daular Larabawa sun yi kokarin ganin an cim ma maslaha cikin ruwan sanyi domin kaucewa zubar da jinni.

Jaridar Al Ahram ta ruwaito cewa akwai ganawa ta musamman da aka yi tsakanin Firaminista Hazem el-Biblawi da ministan tsaro da General Abdel Fattah al-Sisi da Ministan cikin gida Mohamed Ibrahim. Kuma akwai batun da watse magoya bayan Morsi a dandalayensu.

‘Yan uwa Muslmi dai sun jajirce sai an mayar da Morsi ga mukaminsa na shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.