Isa ga babban shafi
Mali

An kammala yakin neman zabe a kasar Mali

A ranar Juma’a ne aka kammala yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na biyu tsakanin ‘yan takara guda biyu Ibrahim Boubacar Keita da Soumaila Cisse da za’a gudanar a ranar Lahadi. Babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban da za’a zaba shi ne gina sabuwar Mali bayan kwashe tsawon watanni 18 kasar na cikin rikici.

Yakin neman zaben 'Yan takarar Shugaban kasa a Mali, Ibrahim Boubacar Keïta da Soumaïla Cissé
Yakin neman zaben 'Yan takarar Shugaban kasa a Mali, Ibrahim Boubacar Keïta da Soumaïla Cissé RFI/Pierre René-Worms
Talla

A zagaye na farko, Tsohon Firaminista Ibrahim Boubakar shi ke da yawan kuri’u kashi 39.7, yayin da Soumaila Cisse tsohon Ministan kudi ya samu yawan kuri’u kashi 19.

Yanzu haka kuma dukkanin ‘Yan takarar guda biyu sun samu linkin magoya baya saboda an yi waje da ‘yan takara 25 a zagaye na farko.

Dukkanin ‘Yan takarar guda biyu sun sha kashi ne a zaben 2002 da Amadou Toumani Toure ya lashe wanda Sojoji suka hambarar da gwamnatin shi a watan Maris din bara karkashin jagorancin Kaftin Amadou Sanago.

Juyin Mulkin sojoji ne ya ba ‘Yan tawayen abzinawa nasarar karbe ikon yankin Arewaci tare da taimakon mayakan Ansar dine da MUJAO.

A watan Janairu ne kuma dakarun Faransa suka kaddamar da yaki domin kwato yankin da ya fada hannun ‘Yan tawaye.

Kasar Mali dai kasa ce mai arzikin Zinari a kasashen Yammacin Afrika amma kasar ta samu kariyar tattalin arziki sakamakon rikicin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.