Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta janye lasisin tono mai na kamfanin Sin bisa zargin gurbata muhalli

Kasar Cadi ta janye lasisin tono mai ga wani kamfani Mai, malakar kasar Sin bisa zargi gurbata muhali. A wata sanarwa da Ministan man fetur ya karanta ta kaffofin yadda labaran kasar,Chadi ta janyewa kamfani tono mai na CNPCIC malakar kasar Sin lasisin cigaba da ayukan shi a kasar.  

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno.
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno. Photo AFP / Bertrand Guay
Talla

A cewar Ministan, Djerassem Le Bemadjiel bincinke ya gano da cewa kamfanin ya gurbata yankin Koudalwa mai nisan kilometa 200 da babban Birnin Djamena wanda ya sa ala’mura suka lalace.

Rahotanni na nuna cewa babbar matsallar da kamfanin ke fuskanta ita ce karanci kayan aiki na tsabtace muhali,domin a koda yaushe ya gudanar da aikin tace mai,akan samu sauran shara mai dauke da guba.

Ministan ya kara da cewa za su shigar da kara domin gurfanar da daukacin magabatan kamfani.

Kasar Chadi na daya daga cikin kasashen da aka fara aikin tono mai a shekara ta 2003,kamar yadda rahotani suka nuna inda akan hako gangar mai 120.000 a ko wace rana tun a shekara ta 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.