Masar
Jami'an tsaron Masar na kokarin kama 'yan Jama'iyyar 'yan uwa Musulmi
Wata sabuwar takaddama ta barke a Masar yayin da jami’an tsaro ke yunkurin cafke wasu magoya bayan jama’iyyar ‘yan uwa musulmi da hambararren shugaban kasar, Mohammed Morsi, wadanda suke boye a wani masallaci dake birnin Alkahira. Wannan lamari na zuwa ne a dai dai lokacin da magoya bayan hambararren shugaban, ke shirin gudanar sabbin zanga zanga a sassa daban daban na kasar.Ko a jiya juma’a, akalla mutane 80 ne suka mutu a wata arangama da aka yi tsakanin bangarorin biyu, lamarin da har ila yau ya yi sanadiyar cafke magoya bayan Morsi su sama da 1000.
Wallafawa ranar: