Isa ga babban shafi
Madagascar

Kotu ta cire wasu ‘yan takarar shugaban kasar Madagasca daga tsayawa takara.

Wata kotun a kasar Madagascar ta cire sunayen wasu ‘yan takarar shugaban kasar da ake takaddama akan su daga cikin jerin sunayen wadanda za su tsaya takara a zaben kasar da za’a gudanar.

Alamar Kotu
Alamar Kotu thisdaylive.com
Talla

Wadannan ‘yan takarar dai sun hada da Andry Rajoelinam da uwargidan Marc Ravamolana, wato Lalao da kuma tsohon shugaban kasar Didier Ratsiraka.

A cewar kotun kasancewar sunayen ‘yan takara cikin wadanda za su yi takara a zaben na kawo tsaiko wajen gudanar da zaben.

A cikin Watan Mayu dai an tantance da ‘yan takara 41 da zasu tsayatakarar shugabancin kasar, amma daga bisani an wancakalar da Sunayen wasu ‘yan takarar da basu cika sharuddan tsayawa takara ba, inji hukumar zaben kasar.

An dai tabbatar da cewar shugabannin kasashe Goma sha Biyar 15 na Kudancin Afruka zasu amince da wannan matakin da Kotun ta dauka a babban Taron sun a wannan shekarar a Maklawi inda al’amarin kasar Madagascar zai kasance dai gada cikin ababen da ke daukar Hankalin Taron.

Yanzu dai ana sa ran cewar za’a gudanar da karbabben zabe a Madagascar, kuma harma kungiyar hadin Kan kasashen Nahiyar Afruka ta yi maraba da matakin da Kotun ta dauka, harma suna karawa da cewar yin hakan zai kasance wata Manuniya ta magance masalar rikicin da ake samu a Madagascar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.