Isa ga babban shafi
Masar

An cafke Jagoran ‘Yan Uwa Musulmi a Masar

Hukumomin Kasar Masar sun sanar da kama shugaban Jam’iyar Yan uwa Musulmi, Muhammed Badie, inda yanzu haka ake tsare da shi a Nasr. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da zub da jini a cikin kasar.

Mohamed Badie Shugaban 'Yan uwa Musulmi a kasar Masar
Mohamed Badie Shugaban 'Yan uwa Musulmi a kasar Masar Reuters
Talla

Cafke shugaban na ‘Yan Uwa musulmi ya kara cusa fargaba da rashin tabbas ga rikicin kasar Masar, inda aka ruwaito kimanin mutane 900 suka mutu sakamakon rikici tsakanin magoya bayan Morsi da Jami’an tsaro.

Ma’aikatar cikin gidan Masar tace an cafke Mohamed Badie ne a kusa da Dandalin Rabaa al-Adawiya inda magoya bayan Morsi ke gudanar da zanga-zanga.

Badie da sauran shugabannin kungiyar ‘Yan Uwa musulmi suna fuskantar zargi ne na hura wutar rikicin kasar Masar bayan Sojoji sun tumbuke Morsi shugaban Dimokuradiyya na Farko a kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kotun kasar ta wanke Mubarak daga zargin cin hanci, kodayake yana ci gaba da zama a gidan yari saboda sauran tuhumar da ake ma sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.