Isa ga babban shafi
Masar

Mubarak na Masar zai fuskanci daurin talala a gidansa

Gwamnatin Kasar Masar tace za’a tsare tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak a gidansa, bayan kotu ta wanke shi daga tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa. Ofishin Firaministan kasar, yace za’a tsare Mubarak ne a karkashin dokar ta-bacin da aka kafa a kasar.

Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak Reuters
Talla

Mubarak zai ci gaba da fuskantar tuhumar da ake masa na hannu wajen kashe masu zanga zangar kin jinin gwamnatin shi a shekarar 2011.

A ranar Lahadi za’a sake sauraren karar Mubarak, kuma a yau alhamis ne ake sa ran za’a sake shi daga gidan yari zuwa gidansa.

Sakin Mubarak na zuwa ne a daidai lokacin da Masar ke cikin rikici tun da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi shugaban Demokuradiyya na farko a kasar.

Rahotanni a kasar sun ce kimanin mutane 1,000 ne aka kashe bayan Jami’an tsaro sun tarwatsa sansanin magoya bayan Morsi da ke neman a dawo da shi saman madafan iko, kuma akwai Magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi da ake tsare da su cikinsu harda jagoran Jam’iyyar Mohammed Badie.

Duk da barazanar da magoya bayan Morsi ke fuskanta amma sun yi kiran gudanar da gagarumar zanga-zanga a gobe Juma’a domin adawa da yadda ake cafke shugabannnsu tare da neman a mayar da Morsi saman madafan iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.