Kenya-ICC
Mahawarar ficewa daga kotun ICC a kasar Kenya
Majalisar kasar Kenya za ta fara mahawara dan ficewa daga kotun hukunta manyan laifufuka.
Wallafawa ranar:
Talla
Zaman Majalisar na zuwa ne gab da lokacin da kotun ke shirin fara shari’ar mataimakin shugaban kasar a makon gobe.
Mataimakiyar shugaban Majalisar kasar, Joyce Laboso ta bada umurnin dawowar Majalisar daga hutu dan mahawara a kai gobe alhamis.
Tuni kotun ta fara tuhumar mataimakin shugaban kasar, William Ruto da laifin hannu a tashin hankalin da yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,100 bayan zaben shekarar 2007.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu