Isa ga babban shafi
Libya

Piraiministan kasar Libya da ya kubuta, ya isa a Hedikwatar gwamnatin kasar.

Piraiministan kasar Libya Ali Zeidan ya isa a Hedikwatar Gwamnatin kasar bayan da ya samu kubuta daga Hannun 'yan Bindiga masu garkuwa da shi.  

Sequestro do primeiro-ministro Ali Zeidan
Sequestro do primeiro-ministro Ali Zeidan REUTERS/Denis Balibouse/Files
Talla

Piraiminista Ali Zeidan dai ya kasance ne a Hannun wasu ‘yan Bindiga da suka kama shi suka kuma ci gaba da yin garkuwa da shi har na tsawon Awanni.

Ya kuma samu tarbo daga manyan ‘yan Siyasar kasar Libya da Jami’an gwamnati a babbar Kofar shiga Hedikwatar gwamnatin kasar ta Libya.

An dai bada labarin cewar Piraiministan na cikin koshin Lafiya ya kuma kama daga Hannu yana godya ga masu yi masa maraba da zuwa.

Wani lokaci ne dai aka shata Piraiministan zai jagoranci babban taron Majlisar zartaswar kasar Libiya dab a sabon ba.

Kasar Libya dai ta fada cikin halin tashin Hankali ne tun baya fadan daya tunbuke tsohon shugaba Mu’ammar Ghaddafi da gwamnatin sa bisa jagorancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.