Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan tawayen M23 za su kulla yarjejeniyar sulhu da gwamnatin Congo

Gwamnatin Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo da ‘Yan tawayen M23 ana sa ran za su amince da wata yarjejeniya ta zaman lafiya a yau Litinin, a wani mataki da ake fatar zai kawo karshen rikicin kasar da aka kwashe shekaru ana gwabza yaki.

Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo  Joseph Kabila
Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo Joseph Kabila Reuters
Talla

Bayan dakarun Sojin Congo sun samu galaba a kan ‘Yan tawayen a makon jiya, ana sa ran ‘Yan tawyaen za su sa hannu a wata yarjejeniya ta zaman lafiya a kasar Uganda.

Akwai daruruwan ‘Yan tawayen da suka mika wuya a kasar Uganda, kuma ana sa ran yarjejeniyar za ta kunshi samar wa ‘Yan tawayen makoma.

Wasu ‘Yan tawayen kimanin 100 ne suka tsallaka zuwa Rwanda.

An dade kuma Majalisar Dinkin Duniya tana zargin kasashen Uganda da Rwanda akan suna taimakawa ‘Yan tawaye.

Kungiyar bayar da agaji ta kasar Birtaniya wato Oxform, ta ce har yanzu tana da shakku a game da kawo karshen yakin basasa a jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, tana mai yin kira ga kasashen duniya su samar da mafita ta siyasa domin samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar.

A wani bayani da ta fitar a yau, kungiyar ta bayyana cewa har yanzu akwai kungiyoyin da ke dauke da makamai fiye da 30 a Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, wanda ke nuni da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.