Isa ga babban shafi
Masar

An kafawa ‘yan jam’iyar ‘Yan uwa musulmi sharadi kamin amincewa da tayin tattaunawa

Wani Minista a kasar Masar ya bukaci ‘ya’yan Jam’iyyar ‘yan Uwa Musulmi da su amince da cewar kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi da Soji suka yi juyin mulki ne, kamin hukumomin kasar su amince da tattaunawa da su.

Shugaban riokn kwaryar kasar Masar
Shugaban riokn kwaryar kasar Masar
Talla

Rahotannin baya-bayan nan sun bayyana cewar daukacin bangarorin biyu wato bangaren Gwamnatin Sojin kasar, da na ‘yan Uwa Musulmi, na ban Hannun Makafi da juna ne kan abinda ya shafi batun tattaunawa tsakanin su.

Tun bayan da aka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi dai akalla an kashe magoya bayan ‘yan Uwa Musulmi 1,000 aka kuma kama wasu dubbai.

Ministan kula da walwalar jama’a na kasar Ahmad El-Borei, ya ce ya zama wajibi a amince cewar kifar da Gwamnatin shugaba Muhammad Morsi na ran 30 ga Watan Yuni, cikakken juyin mulki ne, kuma soji a wannan lokacin sun kifar da shi ne sakamakon zanga-zangar da aka yi da kuma ta girgiza kasar.

A cewar wannan Ministan lallai ne ga Jam’iyyar ‘yan Uwa Musulmi su nemi ahuwa su kuma dakatar da fada.

Yanzu haka dai babu kwanciyar hankali a kasar ta Masar, ko da yake, Gwamnatin rikon kwaryar Sojin ta bayyana a karara cewar ta kifar da gwamnatin ‘yan Uwa musulmi ne domin samar da kwanciyar hankali ga al’ummmar kasar Masar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.