Isa ga babban shafi
Benin

Kotun Faransa ta ki tasa keyar wani dan kasar Benin domin fuskantar shari'a

Wata kotun kasar Faransa ta ki amincewa da bukatar hukumomin Jamhuriyar Benin na tasa keyar wani dan kasuwar kasar, Patrice Talon zuwa gida, saboda fuskantar tuhumar zargin sanyawa shugaba Boni Yayi guba a abinci.

Shugaban kasar Benin, Boni Yayi
Shugaban kasar Benin, Boni Yayi REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

An dai zargi dan kasuwar kuma tsohon na hannun daman shugaban ne da aikata laifin a watan Oktoba na bara, inda ya gudu daga kasar zuwa Faransa.

A cikin makon da ya gabata ne alkalin kotun kasar ta Benin wanda a can baya kotunsa ta yi watsi da wannan zargi da ake yi wa Talon, ya gudu daga kasar zuwa Amurka inda ya nemi mafakar siyasa, yana mai zargin gwamnatin kasar da tursasa masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.