Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shugabannin kasashen Duniya 53 ne zasu halarci Jana’isar Mandela

Kawo yanzu, Shugabannin kasashen Duniya 53 ne suka tabbatar da cewar za su halarci jana’izar da za'a yi wa tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu kuma dan gwagwarmaya Nelson Mandela, jana'izar da za'a gudanar a ranar lahadi mai zuwa.

Hoton Nelson Mandela
Hoton Nelson Mandela Kim Ludbrook
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Afruka ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane ya tabbatar da cewa daga cikin shugabannin har da Barack Obama na Amurka, da Dilma Russeff ta Brazil da Francois Hollande na kasar Faransa, da David Cameron na Burtaniya, yayin da wata majiya ke cewa Raul Castro na kasar Cuba ma, zai halarci jana’izar.

Tsohon shugaban kasar Afruka ta Kudu Nelson Mandela dai ya rasu ne a ranar 5 ga Watan Disamba, bayan da ya yi fama da Jinya, ya kuma rasu ne a Gidan sa.

Daukacin Duniya dai ta shiga zaman makokin rasuwar tsohon shugaban kasar Mandela, wasu daga cikin kasashen ma, sun ayyana Ranakun makoki a kasashen nasu.

Kasar India musamman ta ayyana kwanaki 5 na makokin rasuwar Mandela, tare da sassauto Tutar kasar zuwa rabi, a dukkanin sassan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.