Compaore na sa ran sake tsayawa takara a 2015.
An gudanar da bukukuwan cikon shekaru 53 da samun yanci a garin Dori dake kasar Burkina Faso cikin halin rashi sani tabas dangane da makomar kasar a shekara ta 2015,yayi da yan siyasa ke ciggaba da bayana korafin su ga abinda suka kira yiwa dimokradiya targade da Shugaban kasar Blaise Compaore ke shirin aikatawa.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Burkina Faso Balise Conpaore a jiya alhamis ya bayyana aniyar sa na kiran zaben raba gardama a kasar, domin kawo gyaran fuska ga ayar doka mai lamba 37 dake kumshe cikin kundin tsarin mulkin kasar, da ta kayyade wa’adin shugabancin kasar sau biyu ba kari, domin samun damar sake tsaya takara a jere a shekara ta 2015.
Blaise Compaore,Shugaban kasar Burkina Faso ya hau madafin ikon kasar ne tun a shekara ta 1987,bayan wani juyin mulkin da yayi sanadiyar mutuwar tsohon Shugaban sojin kasar Thomas Sankara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu