Isa ga babban shafi
Madagascar

An kammala yakin neman zaben shugaban kasa a Madagascar

A gobe Juma’a ne Mutanen kasar Madagascar za su kada kuri’ar zeben shugaban kasa zageye na biyu tsakanin Likita Robinson Jean Louis, da Hery Rajaonarimampianina zaben da ake fatar zai kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Robinson Jean Louis da Hery Rajaonarimampianina 'yan takarar shugaban kasa a Madagascar
Robinson Jean Louis da Hery Rajaonarimampianina 'yan takarar shugaban kasa a Madagascar RFI/Marie Audran
Talla

‘Yan takarar biyu sun gudanar da gangamin yakin neman zabensu na karshe a birnin Antananarivo, a gaban dubban magoya bayansu, kwana biyu kafin gudanar da zaben

Tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana da ke zaman gudun hijira a kasar Afrika ta kudu tun bayan kifar da mulkinsa a 2009, ya yi tsokaci ta wayar tarho daga birnin Johannesburg inda yace matsalar cin hanci da rashawa da ta mamaye kasar wani sabon juyi ne aka samu a tarihin kasar ta Madagascar, inda ya kara da cewa, za su sake gina sabuwar kasa mai diyauci, tare da sake maido martaba da darajar al’ummarta

A lokacin yakin neman zaben Jean Luis ya bayyana cewa matakin farko da zai dauka da zarar an zabe shi shi ne, sake dawowa da tsohon shugaban kasar gida, tare da yin kira ga mahukuntan kasar na yanzu da cewa kar su kuskura suce zasu karkata sakamakon zaben.

Shi kuma shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Andre Rajoelina, ya kasance ne wasu a wani filin kwallon zari ruga, inda gwanin nasa Hery Rajaonarimampianina ya gudanar da yakin neman zabensa na karshe, al’amarin da ya sabawa dokar da ke haramtawa shuwagabanin gwamnatin rikon kwaryar, da nuna goyon bayan daya daga cikin yan takarar guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.