Isa ga babban shafi
Kenya-ICC

ICC bata da cikakkun shaidun da za ta gurfanar da Kenyatta

Babbar mai shigar da kara ta kotun duniya da ke hukunta manyan laifufuka ta duniya Fatou Ben Souda, ta ce babu kwararan hujjojin da ke bayar da damar hukunta shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a gaban kotun.Shi dai shugaba Kenyatta, kotun na zargin sa ne da hannun wajen tayar da rikici, bayan kammala zaben kasar da aka gudanar a shekara ta 2007 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu daya.Ben Souda ta bayyana hakan ne bayan da wani da ya kamata ya bayar da shaidar cewa shugaban kasar ta Kenya da hannu wajen tayar da wanan rikici ya yanke shawarar janyewa aniyarsa ta fadar abin da ya sani a game da batun, yayin da wani mutum da ya bayar da shaida a can baya, ya fito fili ya ce abin da bayyanawa masu bincike na kotun karya ce tsagwaronta.Fatou Ben Souda ta ci gaba da cewa, ta la’akari da wadannan hujjoji, ya zama wajibi a gare ta ta fito fili ta bayyana cewa kotun ba ta da kwararan dalilan da za ta dogara da su domin ci gaba da shari’ar ta Uhuru Kenyatta.To sai dai, ta ce za su ci gaba da aikin neman sabbin shaidu ko kuma dalilai kan wannan batu, kuma da zarar aka sami sauyi za su sanar da duniya.A ranar 10 ga watan Satumbar da ya gabata ne dai kotun da ke birnin Hauge, ta soma shari’ar mataimakin shugaban kasar ta Kenya William Ruto, wanda shi ma ake tuhuma da hannu wajen tayar da wannan rikici na shekara ta 2007, yayin da ake jiran kotun ta kammala tattara shaidu domin gurfanar da shugaban kasar da kansa. 

Babbar mai gabatar da kara ta kotun duniya ICC, Fatou Bensouda
Babbar mai gabatar da kara ta kotun duniya ICC, Fatou Bensouda AFP/Emmanuel Dunand
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.