Isa ga babban shafi
Libya

Soja daya ya rasa ransa a ricikin Libya

A kasar Libya soja daya ya rasa ransa yau, wani farar hula daya kuma ya sami mummunar rauni sakamakon tashin ban a da aka dasa cikin mota a gabashin birnin Bengazhi.

Wasu dakarun kasar Libya dauke da makamai
Wasu dakarun kasar Libya dauke da makamai
Talla

Majiyoyin kula da lafiya sun tabbatar da aukuwan lamarin. Bayanai na cewa sau biyar aka harbi sojan kiafin ya mutu.

Tun kawar da Gwamnatin marigayi Moammar Ghaddafi ne dai ake samun munanan hare-hare musamman a wannan gari. Benghazi kuma ya kasance garin da aka fi kai hare hare wanda yake mamaye da mayakan sa kai dake dauke da makamai tun lokacin juyin juya halin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.