'Yan uwa Musulmi sun yi watsi da matakin Gwamnatin Masar
Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ta kasar Masar ta yi watsi da matakin hukumomin kasar da suka bayyana ta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda tare da haramta wa magoya bayanta damar shirya zanga-zanga ko kuma taron gangami.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Masar ta dauki wannan matakin ne bayan wani hari da aka kai a ginin ‘Yan sanda a birnin al Kahira.
Amma Daya daga cikin manyan jami’ai a jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi mai suna Ibrahim Munir da ke guddun hijira a birnin London, yace duk da wannan mataki na gwamnati, magoya bayansu za su ci gaba da tarzoma har sai an mutunta zabin jama’a a kasar.
Wannan matakin zai kara hura wutar rikicin kasar Masar inda darururwan mutane suka mutu tun lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a watan Yuli wanda shi nene shugaban Dimokuradiya na farko a Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu