Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Ministan harkokin wajen Faransa na ziyara a yammacin Africa

Ministan Tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian na wata ziyara kasashe uku dake yammacin Africa yanzu haka, domin ganin nasarar da aka samu a yankunan da sojan kasar suka kai dauki.Ministan na ziyarar kasashen Mali, Niger da Tchadi, don cimma wannan manufa.Shekara daya kenan dai sojan kasar Faransa suka taimaka wajen kawar da ‘yan tawaye da suka kwace Arewacin kasar Mali daga hannun ‘yan tawaye da suka mamaye yankin.Ministan tsaron ya fara kai ziyara ne yankin garin Gao kafin ganawa da Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubakar Keita.A can baya dai, musamman cikin watan uku na wannan shekarar mai karewa, Ministan ya kai irin wannan ziyara zuwa yankin Gao inda ya yabawa Dakarun dake aikin Koran ‘yan tawayen, musamman sojan kasar Chadi dake cikin fafatawan.A wancan lokacin Sojan Faransa sun shaidawa Ministan cewa sun kashe ‘yan tawayen 150 a fada gaba-da-gaba da aka gwabza.Suma sojan Chadi sun shaidawa Ministan cewa sun kashe ‘yan tawaye 150, amma kuma an kasha masu mutane 25.An nunawa Ministan irin kayan fada da aka kwace daga hannun ‘yan tawayen. 

Wasu Sojan Faransa, da ke aiki a kasar Mali
Wasu Sojan Faransa, da ke aiki a kasar Mali AFP PHOTO/PHILIPPE DESMAZES
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.