Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Djotodia Shugaban Afrika ta tsakiya ya yi murabus

Taron Shugabanin kasashen yankin Tsakiyar Afrika da aka gudanar a kasar Cadi ya yaba da murabus din shugaban rikon kwariar Afrika ta Tsakiya da Firaministan sa. 'Yan kasar da dama ne suka bayyana matukar farin cikin su jim kadan da bayar da wanan sanarwa a kasar ta Cadi.  

Michel Djotodia, Tsohon Shugaban riko na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Michel Djotodia, Tsohon Shugaban riko na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Talla

Shugabanin sun gayyaci daukacin ‘yan majlisar dokokin Afrika ta Tsakiya, domin tattauna yadda za a shawo rikicin kasar.

Ana gab da cimma nasara a cewar Sakataren Kungiyar kasashe Afrika ta Tsakiya Ahmed Allami bayan ajiye mukamin shugaban rikon kwaryar kasar Michel Djotodia da Firaministan sa Nicolas Tiangaye.

Bayan tattaunawa da ‘yan majalisar Shugabannin, sun bayyana damuwar su kan yadda hukumomin birnin Bangui, suka gagara kawo karshen zubar da jinin da ake yi a kasar.

Tattaunawar tsakanin bangarorin biyu, ta samar da mafita kan rikicin da ya barke tsakanin ‘yan tawayen kasar, da akasarin su musulmi ne tsiraru, da kiristoci masu rinjaye.

Kamar yadda yake rubuce a kudin tsarin mulkin kasar, kwamitin rikon kwaryar kasar na da kwanaki 15 domin sake gudanar da zaben sabon shugaban kasar.
Sai dai Faransa na ci gaba da sa matsin lamba ga kwamitin domin ya hanzarta zaben sabon shugaban.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.