Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

An rantsar da sabuwar shugabar Africa ta Tsakiya

Yau Alhamis aka rantsar da sabuwar shugabar kasar Africa ta tsakiya, Catherine Samba Panza, da ake fatan za ta kawo karshen tashe tashen hankulan kablanci da suka dabaibaye kasar. Anan kuma fatan shugabar zata fuskanci matsaloin da saka afka wa kasar sakamakon tashe tashen hankulan, da suka faro a shekarar da ta gabata.Catherine Samba Panza mai shekaru 59 a duniya, ta karbi rantsuwar aiki ne daga alkalin wata kotun Majistare, a bikin da aka yi a zauren majalisar dokokin kasar.Samba Panza ta maye gurbin Michel Djotodia, da kungiyar ‘yan tawayen saleka, da akasari musulmi ne suka dora a matsayin shugaban kasar, bayan wani juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Fancois Bozize a watan maris din shekarar bara.Ana sa ran Samba Panza, da ita ce macen farko da za ta jagoranci kasar mai fama da talauci, za ta gaggauta nada Priminista, watakila a cikin daren gobe juma’a, da fatan kafa gwamnati a farkon mako mai zuwa.Ana ganin kafa sabuwar gwamnatin zai taimaka mata wajen fuskantar kalu balen da kasar ke ciki.Sabuwar shugabar tace za ta mayar da hankali wajen gaggauta dawo da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya a kasar, ta Africa ta tsakiya.Rikicin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wasu dubu 400, kimaminin rubu’in alummar birnin Bangui kuma, suka tsere daga gidajen su. 

Sabuwar shugabar Africa ta tsakiya Catherine Samba Panza
Sabuwar shugabar Africa ta tsakiya Catherine Samba Panza
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.