Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Kwamandan sojan Faransa ya ce Anti-balaka na hana ruwa gudu

Babban kwamandan askarawan Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Janar Francisco Soriano, ya ce kungiyar Kiristoci ta Anti-Balaka na yi wa shirin dawo da zaman lafiya a kasar kafar angulu.

Mayakan sa-kai na Anti-Balaka
Mayakan sa-kai na Anti-Balaka REUTERS/Joe Penney
Talla

Janar Francisco wanda ke ganawa da shugabannin addinai a birnin Bangui, ya ce kungiyar na a matsayin mai adawa da duk wani kokari da kasashen duniya ke yi domin wanzar da tsaro a kasar.

Kalaman na kwamandan sojojin Faransa na zuwa ne kwana daya bayan da aka harbe wani dan Majalisar dokokin rikon kwaryar kasar Jean-Emmanuel Njarawa, kisan da ake zargin Anti-balaka da aikatawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.