Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia: Mutane 7 sun mutu a harin al Shebab

Mayakan Kungiyar al Shebab sun dauki alhakin kai harin bom a cikin wata mota da ya kashe mutane 7 a birnin Mogadishu a yau Alhamis. Kungiyar dai ta kai harin ne a kusa da hedikwatar Jami’an tsaro.

Sojojin Somalia sun tsaya a kusa da inda aka kai harin Bom a mota a garin Mogadishu.
Sojojin Somalia sun tsaya a kusa da inda aka kai harin Bom a mota a garin Mogadishu. REUTERS/Omar Faruk
Talla

Kungiyar al Shebab ta dade tana kai hare hare a gine ginen gwamnati saboda adawa da shugabannin kasar da ke samun goyon bayan kasashen yammaci.

Kakakin kungiyar Abdul'aziz Abu Musab ya tabbatarwa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa su suka kai hari a Mogadishu domin karyata ikirarin gwamnati game da  samun nasara akansu.

Rahotanni dai sun ce bom din ya tashi ne tare da wani da ke tukin motar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.