Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Sauraren karar Pistorius a rana ta uku

A ci gaba da sauraren karar Oscar Pistorius, dan tseren guragu da ake tuhuma ya bindige burdurwarsa a gidansa, shedu na uku da aka gabatar a kotu tace ta ji karar hayaniya da hargitsi ne mai nasaba da fada a cikin dare kafin jin karar harbin bindiga.

Oscar Pistorius  a cikin zauren kotu a Pretoria
Oscar Pistorius a cikin zauren kotu a Pretoria REUTERS/Themba Hadebe/Pool
Talla

A zaman sauraren karar Pistorius, an saurari bahasi ne daga shedu guda uku da ke makwabtaka da dan tseren gudun guragun a birnin Pretoria.

A zama na biyu a jiya talata, Estelle Van Der Merwe makwabiyar Pistorius tace hargitsi ne ya tashe ta daga bacci, kuma an kwashe tsawon sa’a daya tana jin karar sabani a gidan Oscar Pistorius a ranar masoya da ya bindige mudurwarsa Reeva Steenkamp.

Tuni dai Pistorius ke kalubalantar tuhumar da ake masa akan bindige budurwasa yana mai ikirarin ya yi harbin harsashen bindiga ne, yana mai tunanin wani ne ke kokarin abkawa a gidansa, a lokacin da budurwarsa ke kwance a saman gado.

Amma bayanan da shedu suka gabatar shi ke kara gasgata zargin da masu gabatar da kara suka yi wa Pistorius akan ya kashe budurwarsa ne bayan samun sabani a tsakaninsu kafin harbin bindiga.

A yau ne aka shiga kwana na uku a ci gaba da sauraren karar Oscar Pistorius a birnin Pretoria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.