Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kashe dimbin mutane a Bentiu

Wani rahoton da MDD ta fitar ya zargin magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riekc Machar da kashe daruruwan mutane akan dalilai na kabilanci, lokacin da suka kwace birnin Bentiu daga hannun dakarun gwamnati a cikin makon da ya gabata.  

Sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Bentiu
Sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Bentiu RFI/Stéphanie Braquehais
Talla

Rahoton na MDD ya bayar da misalai da dama da ke tabbatar da cewa an kashe jama’a a kan dalilai na kabilanci ko kuma addini, inda ya ce bayan da suka kwace garin Bentiu daga hannun dakarun gwamnati, ‘yan tawayen sun afkawa wuraren ibada wato masallatai da kuma coci inda suka kashe jama’a dama.

Rahoton ya ce a babban masallacin birnin kawai an kashe akalla mutane 200 da suka fake a cikinsa tare da raunata wasu fiye da 400, yayin da aka kashe wani adadin a cikin coci da kuma wani asibiti da hukumar abinci ta MDD ta kafa.

Har ila maharan sun yi amfani da gidajen rediyo domin yin kira ga magoya bayansu da su tilsatawa abokan hamayya ficewa daga garin, tare da karfafawa jama’a aikata fyade akan matan da suka fito daga kabilun da na su ba.

To sai dai rahoton ya ce dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa sun samu nasarar kwashe akalla mutane dari biyar daga birnin kuma mafi yawansu sun samu raunuka a lokacin wannan fada da aka gwambza tsakanin dakarun Salvakirr dan kabilar Dinka da kuma tsahon mataimakinsa Rieck Machar wanda ya fito daga kabilar Nuer.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.