Isa ga babban shafi
Algeria

‘Yan bindiga sun kashe Sojojin Algeria 11

Wasu ‘Yan bindiga sun kai wa Sojojin Algeria harin kwantar bauna inda suka kashe Sojoji 11 tare da raunata wasu da dama kamar yadda rundunar sojin kasar ta tabbatar, wannan kuma shi ne hari na farko da aka kai bayan Shugaban kasa Abdelaziz Boutefilika ya lashe zabe wa’adi na hudu.

Jami'an tsaron kasar Algeria
Jami'an tsaron kasar Algeria AFP PHOTO/FAROUK BATICHE
Talla

Ma’aikatar tsaron kasar tace harin ya faru ne a yankin Kabylie mai fama da rikici wanda ke gabas da garin Algiers.

Sanarwar ma'aikatar tsaron kasar tace, an abkawa tawagar sojojin ne lokacin da suke dawo wa daga wani aiki. Yanzu haka sojoji sun ce suna farautar wadanda suka aikata kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.