Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta sake yanke wa ‘Yan Uwa Musulmi hukuncin kisa

Alkalin Kotun da ya yanke wa daruruwan magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi hukuncin kisa ya sake gabatar da wani hukuncin kan Shugaban Jam’iyyar ‘Yan Uwa musulmi Mohammed Badie da wasu mutane 682.

Wani Magoyi bayan Jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ya cinnawa hoton Abdel Fatah al Sisi wuta babban hafsan sojin kasar da ya jagoranci hambarar da Morsi
Wani Magoyi bayan Jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ya cinnawa hoton Abdel Fatah al Sisi wuta babban hafsan sojin kasar da ya jagoranci hambarar da Morsi REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Kotun ta kama Badie ne da sauran magoya bayan Morsi da laifin kisa da yunkurin kisan ‘Yan sanda a kudancin Minya a ranar 14 ga watan Agusta, ranar da ‘Yan sanda suka kashe daruruwan magoya bayan ‘Yan uwa Musulmi a birnin al Kahira.

Yousef Sabry, shi ne Alkalin da ya yanke hukuncin na yau Litinin da kuma hukuncin da ya yanke akan magoya bayan Morsi 529 a watan Maris.

Tun lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a watan Yulin bara, ake ci gaba da tarwatsa ayyukan Jam’iyyar ‘Yan uwa Masulmi a Masar.

Hukuncin akan daruruwan mutane ya janyo suka daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama.

Dangin mutanen da aka yanke wa hukuncin sun mamaye harabar kotun a cikin wani hali na bakin ciki suna masu sukar hukuncin a matsayin zalunci akan ‘Yan uwansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.