Isa ga babban shafi
Najeriya

Michelle Obama ta fusata game da sace 'yan matan Chibok

Matar shugaban Amurka Michelle Obama, ta bayyana sace ‘yan matan da aka yi a garin Chibok da ke jihar Bornon Tarayyar Najeriya da cewa ‘’ aiki ne na assaha’’ sannan kuma wani salon ta’addaci domi hanawa ‘yan matan damar samun ilimi.

Michelle Obama na kira da a dawo da 'yan matan Chibok
Michelle Obama na kira da a dawo da 'yan matan Chibok divulgação/Casa Branca
Talla

Michelle wadda ke gabatar da jawabi a makwafin wanda Obama ke gabatarwa a kowace asabar, ta bayyana sace ‘yan matan a matsayin lamarin da bai kamata kasashen duniya su kawar kai akansa ba, tana mai cewa ita da mijinta Obama, suna a cikin damuwa tun daga lokacin da suka samu labarin cewa an sace wadannan ‘yan mata fiye da 200.

Matar shugaban na Amurka ta ce wannan ‘’aiki ne na dabbanci wanda wata kungiya ta ‘yan ta’adda ta aikata domin hanawa wadannan mata damar samun ilimi da kuma karya wa mata kwarin gwiwar da suke da shi wajen neman ilimi a rayuwasu’’.

Tun a ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai aka sace wadannan ‘yan mata a garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, yayin da aka sace wasu ‘yan matan 8 a ranar 5 ga watan Mayu a garin Warabe da ke cikin jihar, wanda ya kai adadinsu zuwa 223 da ke tsare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.