Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekau ya nuna ‘Yan Matan da suka sace a Bidiyo

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar shekau ya sake aiko da sakon Bidiyo yana mai ikirarin Matan da suka sace a Chibok sun karbi Addinin Islama tare da nuna hotonsu sanye da hijabi, kuma yace ba zasu sake su ba har sai an saki Mutanensu da Mahukuntan Najeriya ke rike da su.

Hoton 'Yan mata da Kungiyar Boko Haram ta nuna a cikin Sakon Bidiyo da shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ya aiko
Hoton 'Yan mata da Kungiyar Boko Haram ta nuna a cikin Sakon Bidiyo da shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ya aiko AFP
Talla

Sabon sakon bidiyon na Kungiyar Boko Haram da Kamfanin Dillacin Labaran Faransa ya samu, an nuna ‘Yan mata kimanin 130 sanye da hijabi suna karatu a zaune a kusa da bishiya.

Akwai Uku daga cikin Matan suka ce sun karbi Musulunci.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka sace ‘Yan Matan 223 a garin Chibok a Jahar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.