Goodluck Jonathan a Chibok
Ana sa ran Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai kai ziyara a garin Chibok inda Mayakan Boko Haram suka sace ‘Yan mata sama da 200, kuma ziyarar Shugaban na zuwa ne fiye da wata guda da aka yi awon gaba da daliban 'Yan Makarantar Sakandare.
Wallafawa ranar:
Wani babban Jami’in gwamnatin Jonathan ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa shugaban zai kai ziyara Jahar Borno kafin ya nufi birnin Paris na Faransa don halartar taron tattauna tsaron yammacin Afrika da barazanar Boko Haram.
Ziyarar Jonathan a Chibok na zuwa ne a yayin da ya ke fuskantar suka da matsin lamba daga ‘Yan Najeriya da kasashen duniya akan tafiyar hawainiya da gwamnatinsa ke yi wajen kubutar da ‘yan matan da aka sace a ranar 14 ga watan Afrilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu