Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta kaddamar da yaki kan Mayakan Abzinawa

Firaministan kasar Mali, Moussa Mara yace kasar ta kaddamar da yaki kan 'Yan Tawayen abzinawa wadanda suka kai hari a garin Kidal suka kashe mutane 36 a kusa da fadar gwamnatin yankin tare da kuma sace wasu kimanin 30.

Firaminista Moussa Mara a lokacin da ya ke ziyara a yankin kidal
Firaminista Moussa Mara a lokacin da ya ke ziyara a yankin kidal AFP PHOTO / FABIEN OFFNER
Talla

Harin na zuwa a lokacin da Firaministan ya ke ziyara a Kidal.

Firaministan yace ganin yadda 'Yan Tawayen abzinawan suka kaddamar da hare hare a garin na Kidal, yanzu haka kasar Mali ta fada yaki da su domin kawar da ta'addanci a kasar.

Mara yace zasu mayar da martani da ya dace domin murkushe Yan tawayen da ke neman hana ruwa gudu a Yankin bayan an samu kwarya kwaryar zaman lafiya.

Rahotanni sun ce, fadan ya barke ne a kusa da ofishin Gwamnan Yankin Kidal, lokacin da wasu Yan tawaye cikin motoci biyu suka abkawa jami'an tsaro, yayin da Firaminsitan ke ziyara, abinda ya yi sanadiyar kashe jami'an tsaron gwamnati 8 da kuma Yan Tawaye 28.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Mali tace 'Yan Tawayen sun yi garkuwa da wasu fararen hula. Firaministan kuma ya zargi jami'an tsaron Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya da sakaci ganin yadda 'Yan Tawayen suka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.