Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane da dama sun mutu a harin Jos

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA a Najeriya tace kimanin mutane 118 suka mutu a wasu hare haren bama bamai da aka kai a garin Jos babbar birnin Jahar Filato, amma ‘Yan sanda Jihar sun yi ikirarin mutane 48 ne suka mutu.

Tagwayen hare haren bama bamai da aka kai a garin Jos a Najeriya
Tagwayen hare haren bama bamai da aka kai a garin Jos a Najeriya AFP
Talla

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ke fuskantar matsin lamba game da tabarbarewar tsaro a Najeriya ya yi Allah waddai da harin na Jos tare da yi wa ‘Yan Najeriya alkawalin shawo kan matsalar.

Amma hasarar rayuka da aka samu a sabbin hare haren bama bamai da aka kai a biranen Kano da Jos ya sake dasa alamar tamabaya akan Gwamnatin Jonathan game da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Zuwa yanzu babu wata Kungiya da ta yi ikirarin daukar alhakin kai hare haren, amma ana zargin Mayakan Boko Haram da suka addabi yankin arewaci.

Hare haren kuma na zuwa ne bayan sace ‘Yan mata sama da 200 a garin Chibok a Jahar Borno.

Jami’in hukumar NEMA Mohammed Abdulsalam, ya shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa mutane 118 ne suka tabbatar da mutuwarsu a harin Jos, kuma 56 suka samu rauni.

02:05

Rahoton Tasiu Zakari daga Jos

Muhammad Tasiu Zakari

Amma rundunar ‘Yan sandan Jahar Filato ta ce mutane 46 ne suka mutu kuma 45 suka samu rauni a tagwayen hare haren bama baman da aka kai a kusa da wata babbar kasuwa a garin Jos.

Shugabannin addinai a Jihar Filato da ta yi fama da rikici sun yi kira ga al’ummar Jahar su kwantar da hankalinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.