Isa ga babban shafi
Najeriya

Sanusi Lamido ne sabon Sarkin Kano

Gwamnatin Jahar Kano ta tabbatar da Sanusi Lamido Sanusi Tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya a matsayin Sarkin Kano, bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero. Sakataren gwamanatin Kano ne ya bayar da sanarwar ga manema labarai.

Sabon Sarkin Kano Tsohon babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi
Sabon Sarkin Kano Tsohon babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi Sanusiweb
Talla

Da farko an ta yada cewa Ciroman Kano Sanusi Ado Bayero ne babban Da ga Marigayi Ado Bayero aka nada, amma yanzu gwamnatin Jahar Kano ta tabbatar da Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnnan babban Bankin Najeriya a matsayi sarkin Kano na 14.

Masaurautar Kano tana cikin Masarautu masu karfin fada aji a Masarautun kasar hausa a Najeriya

Sanusi Lamido dai jika ne ga Sarki sanusi tsohon Sarki Kano kafin marigayi Ado Bayero.

A ranar Juma’a ne Sarki Ado Bayero ya rasu hayan kwashe shekaru 51 akan karagar mulkin Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.