Isa ga babban shafi
Isra'ila

‘Yan Afrika mazauna Isra’ila sun shiga jayin kin cin abinci

A kasar Isra’ila, daruruwan bakin haure daga nahiyar Afrika, sun shiga yajin kin cin abinci, bayan da ‘yan sanda suka tarwatsa wasu masu zanga zanga a wani sansani da suka kafa akan iyakar kasar ta Isra’ila da Masar.

Bakin haure a kasar Isra'ila
Bakin haure a kasar Isra'ila REUTERS/Baz Ratner
Talla

Tun a karshen makon da ya gabata ne bakin haure wadanda mafi yawansu suka fito daga kasashen Eritrea da Sudan.

Rahotanni sun ce bakin hauren sun yi jerin gwano zuwa kan iyakokin Isra’ila da Masar, suka kuma kafa sansanoni, domin nuna kokwarwsu kan yadda ‘yan sandan kasar ke muzguna musu a matsugubin dake Holot.

A cewar masu zanga zangar, matsugunin da aka ajiye bakin hauren tamkar gidan yari ne, inda suka kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta shiga tsakani domin ganin an sama musu mafaka a kasashen da suke burin su koma.

A dai jiya Lahadi ne ‘yan sanda, suka kori masu zanga zangar daga sansanonin da suka kafa, inda rahotanni ke nuna cewa an yi wata ‘yar arangama da ‘yan sandan, lamarin da yasa aka samu raunuka a bangarorin biyu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai bakin haure da masu neman mafaka sama da dubu 53 a kasar ta Isra’ila, wadanda da yawansu sun shiga kasar ne ta hamadar dake kan iyakar Isra’ila da Masar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.